Don samun damar koyon RSH ta yanar gizo, kuna buƙatar yin rijistar shafinka tare da mu kuma sai kana kan shafin.

 

Learning

 

RSH suna haɗa wasu jerin darussan horarwa guda biyar ta yanar gizo wanda aka kira Al'amuran Kiyayewa wato Safeguarding Matters. Darussan suna amfani da koyo ta misalai don ba da wani labarin wata ƙungiya 'mai zaman kanta wadda ake kira Family Health Frontiers (FHF). A cikin jerin darussan biyar, masu koyo za su samu damar bin ƙungiyar FHF yayin da suke neman zama kungiya mai aminci da kuma tafiyar da ƙaluɓalen Kiyayewa.


Kowane darasi zai kasance tare da sanarwar Kiyayewa wanda zai ba da ƙarin sa ƙaimin koyo har zuwa watanni biyu bayan an gama karanta littafin.


Waɗannan darussa na nufar kwararru da ba na Kiyayewa ba a ƙungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) wadanda suke neman hanya mai sauki ta koyo, don koyon muhimman bayanan gaskiya game da Kiyayewa, samun ilimi, yin abubuwa da kuma samun takardar shaida ta RSH. Kuma kwararru a Kiyayewa za su samu moriyar bayanin fasahar, hanyoyin hadi zuwa kayayyaki masu amfani da kuma dabarun magance kalubalen Kiyayewa da CSOs ke fama dasu. Dukkan waɗanda suke aiki a fannin ci-gaba da taimakon agaji za su samu darussan na da amfani. 

Domin kallon bidioyo mai dauke da rubutacciyar fassara, da take fitowa daga kasa, danna alamar “CC” ta karkashin bidiyon domin kunnawa.
 

Gargadi

Waɗannan karatun suna ƙunshe da abun ciki wanda zaku iya samun damuwa.

Dukkanin darussan guda 5 a na samun su cikin harsunan Faransanci, Amharic, Swahili, Hausa da Larabci.

Darussa 1-4 na samuwa cikin harshen Portuguese

Gabatarwa don Darasi na 1


Al'amuran Kiyayewa Darasi na1: Farawa

Wannan shi ne darasin farko a cikin jeri biyar na koyo ta yanar gizo kan Kiyayewa. Wannan jerin yana gabatar da muhimmiyar ma'anonin Kiyayewa ta labarin Family Health Frontiers (FHF) - wata ƙungiyar farar hula ta ƙasa da suke fama da ainihin matsalolin Kiyayewa.

Rawar da za ku taka ita ce yin hulɗa tare da mambobin ƙungiyar FHF yayin da take aiki don tabbatar da Kiyayewa daga Ci da gumi, Cin zarafi da Barazana ta Hanyar Jima'i na haɗe a matsayin muhimmin ɓangaren sabon shiri.

Sakamakon Koyon

Wannan darasin zai taimaka muku da:
•    Sanin ma'anonin kalmomin Kiyayewa;
•    Fahimtar nauyin Kiyayewa a cikin ƙungiya;
•    Gane muhimmancin halayen wurin aiki a harkar Kiyayewa.

Lokacin karatu: mintuna 30.


Gabatarwa don Darasi na 2

Al'amuran Kiyayewa Darasi na 2: Farawa tare da abokan aiki


A Darasi na 2, masu koyon za su ci gaba da raka FHF, a yayin da suka tura takardun neman kuɗi don wani sabon shiri, kammala binciken kwakwaf wajen Kiyayewa da kuma gano abokan aiki na shirin. Kiyayewa a dukkan gudanar da shiri kuma ana binciken hatsarorin Kiyayewa.

Sakamakon Koyon

Wannan darasin zai taimaka muku da:
•    Fahimci muhimmancin binciken kwakwaf na ƙungiyoyi da abokan aiki wajen Kiyayewa;
•    Gano muhimman ayyukan Kiyayewa dake dukkan matakan shirin don gudanar da shirye-shirye cikin aminci; kuma 
•    Gano buƙatar samun jagoranci da al'adun ƙungiya masu karfi a ƙoƙarin samun nagartattun ayyuka.

Lokacin karatu: Awa ɗaya.

A yayin ƙoƙarin kammala darussan, kuna iya ba da shawarwarinku, tambayoyi da tsokaci game da abubuwan da kuka koya tare da sa'anninku akan Dandalinmu na Yanar gizo na tattaunawa.

Don samun damar koyon RSH ta yanar gizo, kuna buƙatar yin rijistar shafinka tare da mu kuma sai kana kan shafin.

Danna nan idan ba ka da shafi na RSH

Danna nan in da ma kana da shafinka na Cibiyar Kayayyaki da Tallafi RSH

 

Gabatarwa don Darasi na 3

Al’amuran Kiyayewa: Ci gaba da Aiwatar da Shirye-shirye cikin Aminci

Anan za a cigaba da ƙungiyar FHF kan tafiyarsu ta kiyayewa.

Wannan darasin zai magance yadda Kiyayewa take:

  • Shiryawa da yin ziyarar duba aikin kiyayewa na wani abokin aiki da ke aiwatarwa;
  • Taimakawa hukumar da ake haɗin gwiwa da ita tare da shirya taron VIP; da
  • Ba da amsa ga wani korafi da shirya rahoto. .

Lokacin karatu Mintuna 45-60

Sakamakon Koyo

  • Fahimci matakai da ake buƙata a lokacin yin wata ziyarar duba aiki, har da shirin aiwatar da Kariya don gudanar da shirye-shirye cikin aminci;
  • Tallafa yadda ya dace ga wani mai korafin kiyayewa; da bayar da Rahoton wata matsalar kiyayewa da ta faru.
  • Tallafa yadda ya dace ga wani mai korafin kiyayewa; da bayar da Rahoton wata matsalar kiyayewa da ta faru.

 

Al'amuran Kariya Darasi na 4

Al'amuran Kariya Darasi na 4: Magance korafe-korafe

Wannan shi ne darasi na huɗu a cikin jeri biyar na koyo ta yanar gizo kan kariya. Wannan jerin yana gabatar da muhimman ma'anonin kariya ta labarin Family Health Frontiers (FHF) - wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa da ƙungiyar da suke haɗin gwiwa da su Sure Health Africa (SHA) masu fama da ainihin matsalolin kariya.

Rawar da za ka taka ita ce kasancewa tare da tawagar FHF yayin da suke tallafawa wani korafin kariya, aiki tare da wani mai bincike da kuma koyon darussa daga bitar dabi'unsu na kariya na cikin gida.

Sakamakon Koyo:

A wannan darasin za ku cigaba da Family Health Frontiers (FHF) akan tafiyarsu ta kariya. Wannan darasin zai magance yadda kariya take:

  • Samun rahoton wata matsalar kariya da yin binciken farko;
  • Tallafawa tsarin binciken; da kuma
  • Shiryawa da yin bitar kariya ta cikin gida don koyon darussa da inganta dabi'u.

Lokacin karatu Mintuna 45-60

LURA:

Wannan darasin ba koyaswar yadda ake bincike ba ne kuma ba zai baka kayan aikin zama mai bincike ba.

Yana nuna tsarin bincike don taimaka muku da fahimtar matakan da ake bi na yin bincike.

Yana nuna mahimmancin amfani da masu bincike daga waje da yadda za'a shigar da hukumomin shari'ah cikin aminci, misali ‘yansanda.

Sashi na 5

Al’amuran Kiyayewa: Sa ido lura, Kimantawa da Koyo cikin Aminci (MEL)

Anan za a ci gaba da ƙungiyar FHF kan tafiyarsu ta kiyayewa.

Darasin zai magance yadda:

  • Ya kamata a yi la'akari da kuma sanya kiyayewa a ayyukan sa ido lura, kimantawa da koyo a gabadayan shirin; kuma
  • Sa ido lura, Kimantawa da Koyo wato MEL na iya goyon bayan tafiyar kiyayewa na ƙungiya ko shiri.

Lokacin karatu Mintuna 45-60

Sakamakon Koyo

  • San asalin ka'idoji don tabbatar da Sa ido lura, Kimantawa da Koyo wato MEL cikin aminci;
  • Fahimci yadda za'a tattara bayanai akan kiyayewa ta ayyukan sa ido na yau da kullum;
  • Fahimci muhimmancin mahalarta shirye-shiryen kiyayewa, mambobin al'umma da ma'aikatan da suke cikin aikin Sa ido lura, Kimantawa da Koyo wato MEL; da kuma
  • Gano hatsarorin kiyayewa a cikin ayyukan MEL da kuma iya aiwatar da asalin ka'idojin gudanar da MEL cikin aminci don magance waɗannan.